Friday 18 April 2014     17 Jumada Al-sani 1435

Aminiya

A+ A A-

Dillalan shanu sun yi barazanar barin kasuwar Oko-Oba

Alhaji Bello  DanmubaffaSarkin Fulanin kasuwar  shanu  da ke  Oko-Oba a Jihar Legas, Alhaji Bello  danmubaffa  ya ce  muddin  aka ci  gaba da  takura musu a kasuwar,  za su tashi su koma  Jihar Ogun, inda suka sayi fili eka 25.
Ya ce ba za su  bari  ruwan da ya ci abokan zamansu mahauta ya ci su ba, domin baya ga tarin haraji ba a shawarce su ba a yayin da gwamnati  ta sayo motocin daukar nama, lamarin da ya sa suka sayi filin, wanda suke sa ran karawa zuwa eka 60.
Sarkin ya ce sun gayyaci sauran ’yan kasuwar su biyo su a duk lokacin da za su yi kaura, kuma za su ba su fili kyauta. “Mun yi ta kokarin a saukake mana yawan takurawa mu da dabbobinmu, ta hanyar kai kukanmu ga gwamnati, amma an yi banza da mu, saboda haka za mu dauki matakin da muke jin ya dace mu”. Inji shi.
Shi ma shugaban Meyetti-Allah na Jihar Legas, Alhaji Abdullahi Laliga ya ce  wani abin da ya sa har suka sayi  fili a Jihar Ogun shi ne ganin saura wata daya kafin kasuwar ta fita daga  hannun Alhaji Idris Yaro Dogara, har mutum 83 sun rubuta wa gwamnatin Jihar Legas suna neman a ba su kasuwar. “Muddin ba a sake mayar wa kamfanin da ke  kula da kasuwar ba a halin yanzu, mai yiwuwa a sami matsala, in wanda za a ba bai san  harkar dabbobi ba.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin gwamnatin Jihar Legas daga kwamishinan gona, Alhaji Gbolahan Lawal, amma hakan ya ci tura.
Ana dai yanka dabbobi  kusan 2,000 a kullum, bayan dimbin jama’a da ke kasuwaci daban-daban a kasuwar.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited