Thursday 24 April 2014     23 Jumada Al-sani 1435

Aminiya

A+ A A-

Articles

Allah Ya yi wa Hajiya Rabi Hardawa rasuwa

A ranar Laraba 25 ga Satumba ne Allah Ya yi wa tsohuwar ’yar Majalisar Jihar Bauchi Hajiya Rabi Mohammed Hardawa rasuwa. Marigayiyar wadda tsohuwar jami’ar jinya ce da ta yi aiki a jihohin Adamawa da Bauchi, ta rasu tana da shekara 70.
Ta yi karatun firamare a garin Hardawa da babbar firamare a Misau inda kafin ta wuce Sakandaren ’Yan mata (GGSS) ta Dala da ke Kano. Ta kuma je makarantar horar da jami’an lafiya ta Ilorin. Kuma ta halarci makarantar Nas da Ungozoma ta Bauchi, inda ta bar aikin jinya a shekarar 1981 ta shiga harkokin siyasa ta zama ’yar majalisa mai wakiltar Hardawa a Majalisar Jihar Bauchi a 1983, ta kuma sake hawa a 2007 zuwa 2011.
Ta yi aikin asibitin Yola a tsohuwar Jihar Gongola da kuma asibitin Misau da Jama’are, inda ta yi ritaya a matsayin Metron dakin haihuwa na Asibitin kwararru na Bauchi. Ta rasu ta bar yayarta da kuma ’ya’yan wanta, ciki har da wakilinmu na Bauchi Mu’azu Umar Hardawa. An yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada Allah Ya yi mata rahama.


Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited