Alamomin So na Gaskiya: Hanyoyin da zaku gane soyayyar gaskiya
So na gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da kowane masoyi yake burin ya samu daga masoyinsa, domin hakan na karawa alaƙar soyayya armashi da ma’ana. A yawancin lokuta, yana da matukar wahala ka gane alamomin so na gaskiya, musamman idan wanda kake tareda shi yana nuna maka so koda kaɗan ne kuwa. Domin kai tsaye ba zaka gane cewa sonka yake tsakani da Allah ko kuma yana da wata manufa kawai a kanka.
Wannan dalilin ne yasa na zauna na zurfafa bincike domin kawo muku manya manyan alamomin so na gaskiya, a cikin wannan rubutun. Amma ayi sani cewa "Idan masoyinki ko masoyiyarka basa nuna wasu daga cikin alamomin amma kuma suna yin wasu tofa gaskiya ni malamin soyayya ba zan iya ganewa ba, illa iyaka abinda na kawo na alamomin so gaskiya suyi muku jagoranci domin fahimtar waɗanda kuke soyayya dasu.
Wannan sune alamun soyayya ta gaskiya kamar haka:
Nuna Kulawa
Duk wanda yake sonki ko take sonka da gaske zai dinga nuna kulawarsa gameda rayuwarki. Wato komai dake damunki zaki ga yana kokarin ya shawo kansa. Ko ya riƙa tambayarki yadda kike ji sannan zai zauna ya saurareki idan kina da wata matsala. Babu ko shakka duk mai sonka koda yaushe zai kasance cikin kulawa da kai dai dai gwargwado. Kulawa na daga manya manyan alamomin so na gaskiya. Domin kulawa tana nuna cewa kina da muhimmanci a rayuwarsa.
Mutuntawa
Mutumin da yake sonki da gaske ko yaushe a shirye yake ya mutuntaki da baki ƙima koda kuwa baya son abun da kike so. Ba ya raina ra’ayinki ko kuma abinda ya shafeki. Yan magana suka ce mutunci madara, dan haka mutuntawa alama ce daga alamomin so na gaskiya.
Yin Gaskiya
Soyayyar gaskiya tana kunshe da cikakkiyar gaskiya. Domin duk mai sonka ba zaiyi maka karya ba, ko ya dinga boye wani abu. Ko da kuwa gaskiyar na iya zama mai wahala, zai tabbatar da cewa ka san abinda yake zuciyarsa. Sai dai wasu lokutan mai so da gaskiya na iya ɓoye wani abu gudun ɓacin ranka.
Yin Afuwa
Kowane ɗan Adam ajizi ne domin babu wanda baya kuskure, wata rana dole zaki ɓata masa rai, to ina tabbatar miki da cewa in dai yana sonki da gaskiya zai fahimceki sannan zai yi miki afuwa, koda kuwa kowa ya kasa fahimtarki. Afuwa a soyayya tana nuni da alamomin so na gaskiya. Kullum burin mai soyayyar gaskiya shine yaya zan saka ki cikin farinciki da kwadayin son zama dashi.
Goyon Baya
Mutumin da yake sonka da gaskiya yana fatan koda yaushe kayi nasara a rayuwa koda kuwa shi ya faɗi, domin shi a tunaninsa indai kayi nasara shima tamkar yayi ne. Goyon baya na daga alamomin so na gaskiya, shiyasa yan magana ke cewa "So hana ganin laifi" domin mai sonki ko me ake ciki ke zai goyawa baya babu ruwansa da gaskiyarki. Shi dai kawai baya so wani ya sameki ko menene kuwa. Kuma zaki ga ya zama mai karfafa miki gwiwa da kuma goyan bayan dukkan burikanki.
Taimakawa
Duk mai so da gaskiya, shine lamba ɗaya wajen kawo tallafi ga dukkan abinda ke damunki matukar yana da hali. A kowane lokaci kike neman taimako zai kawo miki agaji cikin gaggawa. anda yake son ka zai kasance mai bayar da taimako. Ko bama a soyayya ba taimako nada daɗi, domin duk mai taimakonka gaskiya ba maƙiyinka bane. Don haka kisa wannan a ranki taimako ko agaji alama ce daga alamomin so na gaskiya.
Son Kasancewa Dake
In har mutum yana sonka da gaske, za kiga baya gajiya dake, wato koda yaushe yana jin dadin kasancewa tareda ke. Kuma ko me ake ciki zaki ga yana son farincikinki lokacin da kuke tare. Kuma a shirye yake daya tattauna dake ba tareda gajiya ba.
Daga Ƙarshe Ku Sani
Alamomin so na gaskiya cikin sauƙi zasu iya bayyanuwa ta hanyar kulawa, gaskiya, mutunci, da kuma goyon bayan duk wanda ake so. Idan har kina ganin ko kana ganin wadannan alamomi dana lissafa a sama a tareda wanda kake tareda shi, to akwai yuwuwar yana yin sone da gaske tsakaninsa da Allah yake sonki. Amma duk da haka, yana da muhimmanci kayi nazari kai ma da kyau domin samarwa kanka madafa mai ɗorewa.
Tags
Soyayya