Hotunan Lalle Masu Kyau
Lalle wata kyakkyawar al'adar Hausawa ce wacce ke ƙarawa mata kyawun hannu da ƙafa cike da armashi. Nayi burin a yau zan kawo hotunan lalle masu kyau na kasashe daban-daban domin karuwar matan Hausa.
Yan'mata kiyi sani cewa amfani da lalle ba wai kawai iya ado bane, a'a wata kyakkyawar hanya ce ta bayyana fasaha da adon hausawa. Shin yan'mata kin san cewa kuwa Samari suna bala'in son lalle! habawa! musamman idan kika samu wacce ta iya ta laylaya miki shi a hannunki wallahi zaki sha mamaki idan saurayinki ya gani domin sai ya baki tukuici.
A wannan rubutu nawa, ni manazarciyar Aminiya blog zan tattauna kan muhimmancin yin lalle da kuma kawo miki hotunan lalle masu kyau yar'uwata waɗanda zasu janyo miki ƙarin soyayya daga masoyinki abun alfaharinki. Sannan ina so ki kasance wacce bata da lalaci wajen tabbatar da abinda kika koya a wannan post nawa.
Shin yar'uwata kin san meyasa lalle yake da muhimmanci kuwa?
Yau kam bari na baki labari, Lalle yana da alaka mai karfin gaske da al'adun ƙasashe da dama, musamman a Afirka, Asiya, da kuma kasashen Gabas ta Tsakiya. Domin ana amfani da lalle masu kyau da shi a bukukuwa kamar bikin aure, suna, Eid, da dai sauran lokutan murna. Wannan sana’ar ta lalle ta ratsa al’adun mutane da yawa da zamantakewa, inda a kullum ta Allah da kika sani ake samar da sababbin salon lalle masu kyau da suke jan hankalin mata. Kinga kenan in har masu kawo salon lalle masu kyau a duniya basa ƙarewa kema bai kamata ki gajiya da yinsa ba.
Ga Jerin Salon Lalle Masu Kyau
Ga wasu daga cikin nau’ikan salon lalle da suka shahara a faɗin duniya:
1. Salon Lalle Na Zamani
Salon yan'mata kenan domin wannan na amare ne da yan'mata, ga wasu daga cikin hotunan lalle masu kyau na zamani a ƙasa.
Wannan salon lalle ya haɗa kayan gargajiya dana zamani wato shi irinshi mix ne da kayan lalle guda biyu. Wannan salon yana bayar da tsari mai kyau gashi kuma da sauƙi. Sau da yawa ana yin amfani da 'yan zane masu sauƙi wanda ya haɗa da zanen furanni, taurari, da dai sauran ƙananan zane-zane. Wannan salon lalle ya dace da mata yan ƙwalisa masu son salo mai sauƙi.
2. Salon Gargajiya
Wannan salon bana yaran mata bane, domin shi ya haɗa da nau’ikan lalle masu zurfin tarihi na yan baya kenan, kamar yadda ake gani a bikin aure. Sau da yawa shima lalle ne masu kyau wanda yake haɗawa da zane-zane masu armashi da cikakken ado, kamar irin su shuke-shuke da tsare-tsare masu ma’ana.
Salon gargajiya fa sai wacce ta gwada domin ko yaran matanma suna iya yinsa. Daga ƙasa mun kawo wasu daga cikin hotunan lalle masu kyau na gargajiya domin gwada wa.
3. Salon Larabawa
Salon lallen Larabawa a yawancin lokuta yafi sauƙi, kuma ko ban faɗa ba kin san yana da kyau sosai. Domin yana da zane-zane da aka fi yin su a layi ɗaya ko kuma cikin zanen furanni, wanda yawanci an fi bayyana du a tsakiyar hannu ko ƙafa.
4. Salon Indiyawa
Indiyawa dama abun kwaikwayo ne in dai ta fuskar iya zanen lalle ne domin suna ɗaya daga cikin kasashen da ke da salo mai kyau na lalle. Wannan salo nasu yana da nau'in zanen lalle wanda ke cike da karko da nagarta, irinsa ake cewa maida tsohuwa yarinya, yana cike da haɗin furanni, zoben hannu, da wasu sauran zanuka masu ɗaukar hankali. Shima ga hotunan a ƙasa.
5. Salon Afirka
Wannan Salon Afirka wato na gida kenan, wanda da yawa daga cikin matan hausawa basu cika yinsa ba musamman a wannan zamani. Yana da nau’ikan zane masu zurfi da kuma amfani da manyan layuka masu kauri. Shi irin wannan salon yana bayar da cikakken zane a kan hannu ko ƙafar mace gaba ɗaya, wanda har yanzu matan kudanci ke yinsa sannan shima ya dace da bukukuwa da manyan shagulgula.
Menene amfanin yin Lalle
1. Domin Ado da Kyau: Lalle yana ƙarawa hannu da ƙafar mace kyau, sannan yana jan hankali matuka musamman maza, kuma yana sa mace tayi fice a cikin taro.
2. Al’ada da Tarihi: Yawanci duk zane-zanen lalle suna nuna al'adun gargajiya ne da tarihinsu, hakan yana ƙara sawa ana fahimtar asalinsu.
3. Natsuwa da Jindaɗi: Ta bangaren masu yin zanen lalle kuwa suna matukar jindaɗi da kwanciyar hankali yayinda suke zana shi. Kuma kema wacce aka yiwa zaki ji wata nutsuwa tana sauka a ranki duk lokacin da kika kalli hannu ko ƙafar ki domin suna yin mulai ne.
4. Hanyar Bayyana Fasaha: Lalle wata hanya ce ta bayyana fasaha da kirkire-kirkire ta hanyar zane-zane masu ma’ana. Idan kika duba hotunan lalle masu kyau wanda muka kawo a sama zaki fahimci hakan.
Yan'mata ko Uwargida ku kasance masu yin Lalle: Sannan ku guji:
Yin amfani da duk wani irin lallen mara inganci domin gujewa ƙaiƙayi, kumburi ko wani abu mai illa ga fata.
Ki tabbatar da cewa fatarki tana da tsafta wato kin wanketa sosai kafin yin lalle domin yayi kyau sosai.
Kada ki wanke lalle daga gamawa idan ba haka ba wallahi za'a yi miki dariya "ace baki da sa'ar farin namiji" ki bar shi ya bushe sosai domin zanen ya bayyana yadda ya kamata.
Daga Ƙarshe
Hotunan Lalle Masu Kyau ko bada shawarar yinsa ba, ba wai kawai nayi wannan surutu bane domin ki leƙo gidan sannan kiyi tafiyarki a'a ina so ki gwada sannan ki gode min ni marubuciyar wannan gida; kar ki manta cewa lalle alama ce ta fasaha, al’ada, dake ƙarin kyau. Ko kina son salo mai sauƙi ko kuma salo mai cika hannu gaba-ɗaya, zaɓi ya rage naki yar'uwata akwai nau'ikan lalle da yawa da za su dace da ke.
Tags
Kwalliya