Sakon Barka Da Safiya

Sakon Soyayya Na Barka Da Safiya Domin Masoya:

Sakon Barka Da Safiya

Soyayya tana daya daga cikin kyawawan al’amura, wanda suke faranta zuciyar kowane ɗan-adam, musamman idan ya kasance ana bayyanata cikin shauki da nuna tsantsan kauna. Haba malam ai ba abinda yafi daɗi irin kamar kana farkawa daga bacci kaji saukar Sakon Barka Da Safiya na soyayya mai cike da girmamawa da nuna ƙauna daga masoyiyarka. 

Nasan ko ban faɗa ba yanzu haka kayi murmushi, domin na rantse idan ka samu yarinya wacce tasan sirrin yadda ake tsara sakon barka da safiya na soyayya to kawai ka gama dacewa. Domin duk wani guntun ɓacin ranka wanda ka tashi dashi daga bacci sai dai kawai ka nemeshi ka rasa. Dalilin kuwa shine samun budurwa mai sonka da kayi, domin wacce ke sonka kaɗai ce zata iya zama har ta turo maka sakon barka da safiya.

Ko tantanma babu sau da yawa, daga cikin gajerun sakon da yan'mata kan turowa samarinsu a kowace rana babu wanda yafi burge samari irin sakon barka da safiya. Yar'uwata idan bakya yi to daga gobe ki gwada, ki janyo wayarki da wuri da safe ki tsara ingantattun kalaman soyayya na barka da safiya ki hankaɗawa sahibinki. Na faɗa miki zaki sha mamaki domin a wannan rana ke zaki zamto abar tunaninsa domin dole zaiji kin ƙara shiga ransa. 

Idan kin rasa abinda ya kamata ki rubuta masa na sakon barka da safiya, kar kiyi ƙasa a gwiwa ki garzayo wannan gida namu ki kwafa wanda kika ga yayi miki sannan sai ki ɗan gyarashi yayi daidai da masoyinki ki tura masa. Idan ma kin manta inda wannan rubutu yake kije search bar (Wannan alama 🔍) sai ki rubuta sakon barka da safiya na soyayya, to zata kawo miki wannan rubutu kai tsaye, sai kiyi abinda ya kamata. Mu dai burinmu shine ki zama mace mai kulawa da zata zama silar da ran saurayinta ko mijinta zai fara farantuwa da shiga farinciki a kowace safiya.

A wannan blog post nawa, ni sarkin soyayya na wannan gida, na tattaro muku sakon barka da safiya na masoya wadanda suke bayyana yadda zuciyar masoya take ji dangane da junansu. 

Yauwa kafin in wuce, ina so a fahimci wani abu, wannan rubutu na sakon barka da safiya bawai munyi shine domin yan'mata kaɗai ba, a'a har samari. Kawai dai idan ka kwafa ne sai ka gyara ka mayar dashi a matsayin mace zaka turawa. 

Menene dalilin da yasa Sakon Soyayya Na Barka Da Safiya suke da muhimmanci?

Faranta Ran Masoyi: 
Sakon barka da safiya na masoya suna taimakawa ƙwarai da gaske wajen sanya masoyi fara'a da nishadi tun daga wayewar gari.

Nuna Kulawa: 
Tura wannan sako yana nuna yadda masoyi yake kewar masoyinsa a kowane lokaci, wato kai kana sharar bacci, ita kuwa bata gajiya wajen tunaninka da nuna tsantsan kauna a gareka ba, har zuwa lokacin da ka farka daga bacci. Nan ma kana buɗe ido kayi arba da sakon barka da safiya data turoma.

Kara Dankon Soyayya: 
Tabbas, tura sakon barka da safiya yana matukar raya rayuwar soyayyar masoya, domin hanya ce mai sauki wacce zaku iya amfani da ita domin ƙara dankon aminci da ƙaunar juna a tsakaninku. Kuma ku sani cewa yawan tura sakon barka da safiya na soyayya a kai-a kai na taimakawa wajen kara gina dangantaka mai kyau da nunawa masoyinki cewa kefa mace ce mai juriya.

Waɗannan sune Sakon Barka Da Safiya na soyayya domin ƙara ƙarfin ƙauna:

1.

Wannan sakon barka da safiya namiji zai iya amfani dashi kai tsaye: Na wayi gari cikin soyayyarki annurin zuciyata,
sannan ina cikin kyakkyawan yanayi ne sakamakon soyayyar da kike nunamin a kowane lokaci.

Zuciyata takan tsananta kewarki a duk lokacin da nake maraicin ganinki, Sau da yawa nakan rasa a wace duniya nake ciki duk lokacin dana tuna da tausasan kalaman bakinki.

2.

Sakon barka da safiya wanda mace zata turawa saurayi: Amincin Allah da yardarsa su tabbata a gareka ya kai jarumin jarumai,
Hakika kowacce safiya tana wanyewa ne da sabuwar soyayyarka a zuciyata, hakan yasa kodayaushe nake ƙara godiya ga Allah wanda ya zaɓa mini kai a matsayin abokin rayuwa.

Ina fatan zaka kalli mudubi a lokacin da kake  karanta wannan sako nawa, domin kaga irin baiwar kyau da kirar mazajen gaske da Allah ya kara maka a cikin wannan sassanyar safiyar.

Ni dai babban burina a koda yaushe shine ina fatan sakona ya zamo abu mafi sanya farinciki da ya fara riskarka a wannan rana. Ina Mai Yi Maka Barka Da Safiya.

3.

Tom, shi kuma wannan na maza ne, sakon barka da safiya wannan mai zafi ne: Zuciyata ta cika da godiya ga ubangiji madaukakin sarki da ya bani masoyiya kamarki. Kowane lokaci idan na farka daga bacci, sabon so da ƙaunarki suna ƙara sauka a zuciyata wanda suke kara mini karfin gwiwa.

Fatana Allah ya cika mana burin soyayyarmu, mu kasance ma'aurata kuma ya sanya soyayyarmu ta dore har abada. Barka da safiya masoyiyata.

4.

Sakon barka da safiya na hudu kuma na mata ne: Da kowace safiya idan kaga rana ta ɓullo, to ka san cewa itace alkawarin sabuwar rana da Allah ya bamu.

Kuma idan kaga duhu ya rufe ta to kasan shine ya zamto shaidar soyayyarmu da rana ta haska. Idan har wannan sakon barka da safiya, ya sameka, to kayi sani cewa zuciyata tana tareda kai a kowane sa'i. Ina mai rokon Allah ya albarkaci wannan safiyar ga rayuwarka. Barka da safiya hubbyna.

5.

Wannan sakon barka da safiya na musamman ne, domin kuwa wannan safiya tazo tareda tunaninki da kuma fatan ki samu rana mai cike da farinciki da annashuwa a rayuwarki.

Masoyiyata ina so ki sani cewa, tabbas rayuwata bata da wani alfanu idan babu ke. Ki kasance cikin aminci da amincewa. Barka da safiya.

6.

Habibina ina fatan wannan ingantaccen sakon barka da safiya ya risketa har kan makwancinka, wanda nake fata wata rana zan kasance a kusa da kai.

Kamar yadda wannan safiya take sabuwa, haka sabuwar soyayyarka da kaunarka a kowace rana ke ƙara shigata.

Kana haskaka duniyata kamar yadda hasken ranar wannan safiya ke mamaye duniya cikin nutsuwa. Ina maka fatan alkhairi a wannan sabuwar rana. Barka da safiya.

7.

Sakon barka da safiya na bakwai kuwa na samari ne: Masoyiyata, yau na tashi cikin matsanancin kewarki kamar yadda kullum nake tashi.

A kullum addu'ata ita ce Allah ya cigaba da kare ki daga dukkan mai sharri da mai ƙulle-ƙulle domin raba ni dake.
Ki wuni cikin farin ciki da nishadi daga yau har kullum. Ina miki barka da ganin sabuwar rana.

8.

Wannan karo kuma sakon barka da safiya na maza ne: Son ganin jindadi a tattare dake da kuma son kulawa dake sun zamto tamkar wata gobara mara cinyewa a zuciyata wanda basa taɓa gushewa.

Wannan safiyar ta kara tunatar dani irin ni’imar da ubangiji ya nufa take samun masoyi, musamman idan yana da masoyiya kamar ki.
Ki kasance cikin aminci. Barka da safiya masoyiyata.

9.

Da zarar idanunka sunyi arba da wannan sakon barka da safiya nawa, to ka duba sama kaga yadda hasken rana yake haskaka duniya cikin saiɓi da kwanciyar hankali. To hakika tamkar haka zuciyata take jin haskakawa da farin ciki a duk lokacin da na tuna da kai.

Ina a jikina cewa wannan rana ta musamman ce, kuma ya tabbata zata zama mai albarka a garemu. Barkarki da farkawa shalelena.

Daga karshe masoya ku sani

Sakon barka da safiya kaɗai ba zasu inganta soyayya yadda ya kamata ba, domin soyayya tana bukatar lokaci, kulawa, gaskiya da riƙon amana. Rubuta sakonnin soyayya na barka da safiya ka turawa masoyi yana tabbatarwa masoyi cewa kana kewarsa kuma kewa SO ne. Matukar zaku jajirce wajen yin hakan zaku samu ƙarin dankon zumunci da soyayya a tsakaninku. Nagode

Shin kuna da wata shawara ko wani sako da zai iya ƙara danƙon soyayya? zaku iya rubuta mana a comment section.

Post a Comment

Previous Post Next Post