Addu'ar Janyo Hankalin Saurayi: Yadda Zaki Samu Soyayya Ta Gaskiya:
Soyayya wata kyauta ce daga Ubangiji Allah madaukakin sarki, kuma idan kina son samun masoyi nagari ko kuma ki tsakar da naki, to hanya mafi dacewa ita ce ki dinga yin addu’ar janyo hankalin saurayi. Idan har kina roƙon Allah da zuciya ɗaya, inshallah zai baki wanda yafi dacewa da rayuwarki.
A wannan rubutu nawa na yau ni malamar wannan shafi, zan koyar dake dabaru daban daban har ma kuma na koyar da addu’ar janyo hankalin saurayi kamar yadda Annabi (SAW) da Al-Qur’ani suka koyar, tareda hikimomin da ya kamata ki bi don samun soyayya mai albarka sannan mai ɗorewa.
Muhimmancin Addu'ar janyo hankalin saurayi a Soyayya:
1. Addu’a Tana Kawo Sauki
Idan kina matukar son saurayi amma baki san hanyoyi na yadda zaki jawo hankalinsa ba, to fa addu’a zata miki matuƙar tasiri.
2. Addu’a Tana Sa a Ki Sami Wanda Ya Fi Dacewa
Addu'ar janyo hankalin saurayi bawai iya zaunar da masoyi take ba, a'a, har ma da neman kariya akan wanda kike so idan ya kasance ba alkhairi ne ba. Idan kin roƙi Allah, zai baki wanda zai kula dake da soyayya cikin rikon amana.
3. Addu’a Tana Kare Soyayya
Koda yaushe soyayya bata dorewa sai da albarkar Allah. Yin addu’ar janyo hankalin saurayi tana kare soyayya daga matsaloli kamar yaudara, rabuwa, ko rashin jituwa.
Ga Wasu Addu'o'in Da Zaki Iya Amfani Dasu Domin Janyo Hankalin Saurayi:
Ga wasu addu'o'in da zaki yi domin samun tsayar da hankalin saurayinki a kanki ko neman soyayya mai albarka, daga Al-Qur’ani da Hadisi:
1. Addu'ar Janyo Hankalin Saurayi da harshen Hausa:
"Yaa Allah, idan wannan saurayi alkhairi ne a gareni, ka sa zuciyarsa ta karkata zuwa gare ni cikin soyayya ta gaskiya. Idan ba alkhairi ba ne, ka sauya min da wanda yafi alkhairi a gare ni."
2. Addu’a Daga Al-Qur’ani Domin Samun Kyakkyawar Dangantaka Tsakaninki Da Masoyinki:
Allah ya faɗa wannan addu’a a cikin Al-Qur’ani wadda za ta taimaka wajen samun abokin rayuwa nagari:
رَبِّ هَبْ لِي مِن لَّدُنكَ زَوْجًا طَيِّبًا يَكُونُ قُرَّةَ عَيْنٍ لِي وَيُسَاعِدُنِي فِي دِينِي وَدُنْيَايَ(Rabbī hab lī min ladunka zawjan ṭayyiban yakūnu qurrata ‘aynin lī wa yusā‘idunī fī dīnī wa dunyāyā)"Ya Ubangiji, ka ba ni abokin rayuwa nagari, wanda zai zama abin farin ciki a gare ni kuma zai taimaka min a addinina da rayuwata."
3. Addu’a Domin Allah Ya Sa Masoyi Ya So Ki
اللَّهُمَّ اجْعَلْ فِي قَلْبِهِ مَوَدَّةً وَرَحْمَةً نَحْوِي، وَاجْعَلْنِي قُرَّةَ عَيْنِهِ بِرَحْمَتِكَ يَا أَرْحَمَ الرَّاحِمِينَ(Allāhumma aj‘al fī qalbihi mawaddatan wa raḥmatan naḥwī, waj‘alnī qurrata ‘aynihi biraḥmatika yā arḥamar rāḥimīn.)"Ya Allah, ka sanya soyayya da tausayi a zuciyarsa a kaina, ka sa ni zama abin farin cikinsa, da rahamarka ya Ubangijin rahama."
4. Addu’ar Annabi Yusuf (AS) Domin Samun Karɓuwa
Idan ana son addu'ar janyo hankalin saurayi da samun karɓuwa a idonsa, ana iya yin addu’ar Annabi Yusuf (AS):
فَسَوْفَ يَأْتِي اللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ(Fasawfa ya'tīllāhu biqawmin yuḥibbuhum wa yuḥibbūnahu)"To, Allah zai kawo wata al’umma da zai so su, kuma su ma za su so shi." (Surat Al-Mā’idah: 54)Ana iya karanta wannan ayar tare da roƙon Allah da cewa:"Ya Allah, ka sa wannan saurayi ya so ni da so na gaskiya kuma ka dawwamar da soyayyarmu cikin aminci da albarka."
5. Addu’ar Hana Saurayi Mantawa Da Ke:
اللَّهُمَّ اجْعَلْنِي فِي قَلْبِهِ وَذِهْنِهِ وَاجْعَلْ حُبِّي يَمْلَأُ زَمَانَهُ وَمَكَانَهُ(Allāhumma aj‘alnī fī qalbihi wa dhihnihi, waj‘al ḥubbī yamlā’u zamānahu wa makānahu.)"Ya Allah, ka sanya ni cikin zuciyarsa da tunaninsa, ka sa soyayyata ta cika rayuwarsa da lokutansa."
Abubuwan Da Zaki Yi Domin Ubangiji Ya Karɓi Addu’arki da Sauri:
1. Kiyi Addu’a da Tawakkali
Duk lokacin da kike yin addu’a, ki tabbata kinyi tawakkali ga Allah. Kada ki damu idan baki ga sakamako ba nan take.
2. Ki Nemi Albarka Da Lokutan Da Aka Fi Karɓar Addu’a:
Akwai lokutan da addu’a Tafi karɓuwa, kamar:
Bayan sallar farilla.
A daren Juma’a.
A lokacin sujuda.
Da safe kafin fitowar rana.
3. Ki Guji Haramun
Soyayya ta halal tana samun albarka daga wajen ubangiji. Idan kina son saurayi da gaskiya, ya zama dole ki guji karya, yaudara, ko aikata alfasha.
4. Ki Kasance Mai Kyawawan Halaye
Halin mutum yana da tasiri sosai a soyayya. Idan kina so a addu'ar janyo hankalin saurayi tayi aiki sosai, to yana da kyau ki kasance mai:
Ladabi da biyayya.
Tsafta da kyau.
Mutunci da girmamawa.
Sauran Abubuwan Da Za Su Iya Janyo Hankalin Saurayi
Baya ga addu’ar janyo hankalin saurayi, akwai wasu hanyoyi da zaki iya bi don jawo hankalin saurayi cikin sauƙi:
Yin Kyakkyawar Shiga: Ki dinga yin shiga ta mutunci sannan ki kula da tsafta da yin kyau.
Ki kasance Mai Tausayi da Kyautatawa: Saurayi yana son mace mai tausayi da ladabi.
Yin Magana da Hikima: Ki guji maganganu marasa amfani.
Nuna Daraja da Amana: Mutunci yana ƙarfafa soyayya. Sannan ki kasance mai riƙon amana.
Ki Sani Cewa
Addu'ar janyo hankalin saurayi ba wani abu ne mai wahala ba idan kina yi da gaskiya da kuma kiyaye halayen kirki. Addu’ar janyo hankalin saurayi tana taimakawa masoya sosai wajen samun soyayya ta gaskiya da aminci.
Ki tabbata kina roƙon Allah a kowane hali domin shine Mai bayarwa kuma Mai sauƙaƙa duk wani al’amari.
Tags
Soyayya