Alamomin Karamar Yarinya Na Sonka

Alamomin Karamar Yarinya Na Sonka 

Alamomin Karamar Yarinya Tana Sonka

A yawancin lokuta soyayya abu ne mai rikitarwa, musamman idan aka zo batun fahimtar yadda mace ke nuna soyayyarta. Sau da yawa, karamar yarinya (ko dai ‘yar makaranta ce ko wata yarinya a unguwarku) ba zata fito fili ta fada maka cewa tana sonka ba. Ni kuma malamin soyayya na wannan gida a wannan rubutu nawa mai taken alamomin karamar yarinya na sonka zanyi bayani yadda ya kamata domin ka fahimta cikin sauƙi.

Akwai wasu alamomi da zasu iya nuna maka cewa karamar yarinya tana cike da soyayyarka. Wato ayi sani cewa alamomin karamar yarinya tana sonka daban daban ne, kuma yau inshallah za mu feɗe biri har wutsiya kan yadda zaka gane idan karamar yarinya tana sonka.

1. Yawan Satar Kallonka

Idan yarinya tana yawan kallonka akai-akai ko tana satar kallonka a lokacin da baka lura ba, to hakan yana iya nuna cewa tana da wani abu a cikin zuciyarta gameda kai. Idan kuma ka fahimci cewa tana juya kanta ko ta fara dariya idan ka kamata tana kallonka, to zance na gaskiya akwai yiwuwar tana sonka.

2. Son Zama Kusa da Kai

Na daya cikin alamomin karamar yarinya tana sonka ta dinga neman hanyoyin zama kusa da kai, ko da kuwa ba kai ka fara zaman ba. Wato kawai zaka ga tana so ta zauna kusa da kai kamar a aji ko wani wajen taro, ko ta dinga neman dalili don yin hira da kai, ko ta dinga shiga abubuwan da suka shafeka.

3. Yi Maka Dariya Ko Wasanni

Sau da yawa, yarinyar da take sonka zata so yin ta rinƙa yima wasanni domin kawai taga farincikinka ko tayi dariya da duk abinda ka fada koda bai bata dariya ba. Haka nan, kuma tana iya yin zance ko wasanni da kai domin ta janyo hankalinka.

4. Tana Nuna Maka Kulawa

Na daya daga cikin alamomin karamar yarinya tana sonka yawan nuna maka kulawa, wato za kaga tana nuna damuwa da abubuwan da suke faruwa a rayuwarka. Wani lokacin ma har ta tambaye ka yadda kake ji, ko ta nuna sha’awa ga abubuwan da kake so. Bincike ya tabbatar da cewa nuna kulawa yana daya daga cikin manyan alamomin soyayya.

5. Jin Kunya Ko Yanayinta Ya Canja Idan Kana Wurin

Wannan ma na ɗaya daga cikin alamomin karamar yarinya tana sonka, Idan ka lura da cewa tana yawan jin kunyarka ko ta soma zama kamar bata saba da kai ba idan ka zo kusa da ita, domin hana yana nuna cewa tana jin wani abu a zuciyarta gameda kai. Wannan jin kunya sau da yawa yana da alaƙa da soyayya, musamman ga ‘yan mata masu tsoron bayyana abinda ke zuciyarsu.

6. Aikawa da Sakonni ko Kira Akai-Akai

Idan yarinya tana sonka, za ta nemi hanyar tuntubarka akai-akai ta hanyar sakon waya ko kuma kira. Zata so tasan abubuwan dake wakana a rayuwarka ko ta taya ka magana akan wasu abubuwan da suka shafeka. Koda kuwa wane iri ne.

7. Tuna Maka Da Abubuwan da Ka Faɗa a Baya

Tunatarwa da daga cikin alamomin karamar yarinya tana sonka, wato in dai kuna magana da ita to zata dinga dawo da wasu maganganu naka domin kafa hujja ko nuna maka cewa tana ɗaukar maganarka da muhimmanci. Idan yarinya tana yawan tuna maka wasu kananan abubuwan da ka fada a baya, wannan yana nuna cewa tana kula da duk wani motsinka fiye da kima.

8. Jin Kishi

Idan ka fara magana da wata yarinya ko ka nuna kulawa ga wata macen, to babu shakka yarinyar da take sonka zata nuna alamar kishi wata ma kana ganinka zaka gane a yanayinta. wato hakan na iya bayyananuwa ta hanyar yin shiru, sauya fuska ko nuna rashin jindadi.

9. Son Ta Jawo Hankalinka

Idan yarinya tana sonka, zata iya yin kowane abu domin taga ta jawo hankalinka, kamar canza salon sutura, yin kwalliya sosai ko nuna kwarewarta a wasu fannoni domin ka lura da ita.

10. Yawan Sauraronka

Idan ka lura da cewa yarinya tana sauraranka sosai fiye da yadda take sauraron sauran mutane, to tabbas akwai yiwuwar tana sonka ne, domin hakan na ɗaya daga cikin alamomin karamar yarinya tana sonka, domin hakan na iya zama alamar cewa tana son kasancewa da kai.

Abubuwan da ya kamata kayi idan ka fahimci karamar yarinya tana Sonka:

(*). Ka Girmamata
Abokina idan har ka fahimci cewa yarinya tana sonka, yana da kyau ka girmamata, ka kuma kasance mai mutunci a gareta. Kada kayi amfani da wannan damar domin wulakanta ta ko yin wasa da zuciyarta.

(*). Ka Dinga Hira Da Ita Koda Bata Soyayya Bace
Sakamakon fahimtar alamomin karamar yarinya tana sonka, idan ya kasance kai ma kana da sha'awa gare ta wato kana sonta, to za ka iya fara magana da ita ta hanya mai sauki. Kuma kada ka matsa mata ko ka sa ta jin tsoronka kuma.

(*). Bayyana Mata Ra’ayinka
Idan ka fahimci cewa kai ma kana sonta, babu laifi ka bayyana mata hakan a cikin natsuwa da kulawa. Idan kuwa ba ka da niyya, ka kasance mai mutuntata, ka kuma guji bata mata rai domin mai sonka ba maƙiyinka bane.

(*). Ka Kula da Halinta
Duk da fahimtar kasancewar alamomin soyayya a tattare da ita, yana da kyau ka kula da yadda take mu'amala da jama'a, domin wasu lokutan mutane na iya nuna kulawa kawai ba tareda soyayya ba. Kaga kenan duka alamomin karamar yarinya tana sonka zasu iya kasancewa amma kuma ba sonka take ba kawai yanayinta ne haka a gareka.

Alamomin karamar yarinya na sonka suna da rikitarwa a yawancin lokuta, shiyasa fahimtar alamomin soyayya daga karamar yarinya na bukatar matukar bukatar kulawa da lura da halayenta da kyau. Idan har ba soyayya ce ta kullu ba tofa babu tabbas domin wadannan alamomi basu da cikakkiyar tabbaci, sai dai suna iya taimaka maka wajen fahimtar yanayin da take ciki. Muhimmin abu shine ka kasance mai girmamata da kuma mutunta-ta kowane lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post