Kalaman Barkwanci A Soyayya

Kalaman Barkwanci A Soyayya:

Kalaman Barkwanci a soyayya

Soyayya tana bukatar farinciki da nishaɗi kamar yadda take bukatar kulawa da kuma fahimtar juna. Yin amfani da Kalaman barkwanci a soyayya na ɗaya daga cikin hanyoyin dake ƙarfafa dangantaka tsakanin masoya. Domin kalaman barkwanci a soyayya suna sanya nishaɗi a tsakanin masoya, sannan suna rage damuwa, kuma suna saka soyayya ta cigaba da ɗorewa a rayuwar masoya cike da annashuwa.

A cikin wannan rubutu nawa na yau ni sarkin soyayya, zan tattauna yadda zaka iya amfani da kalaman barkwanci a soyayya wajen ƙarfafa dangantaka, tareda kawo misalan kalmomin da zaka yi amfani dasu masu saka nishadi domin nishaɗantar da masoyiyarka.

Meyasa Kalaman Barkwanci a Soyayya Ke Da Muhimmanci Ga Masoya?

(1). Suna Ƙarfafa Dangantaka:
Lokacin da kake nishadantar da masoyiyarka da kalaman barkwanci, haka yana ƙara kulla sabawa da junanku, da zumunci har ma kuma na kawo jindaɗin kasancewa tare.

(2). Rage Yawan Fada:
Yin amfani da kalaman barkwanci a soyayya na taimakawa wajen rage damuwa da gajiya a cikin dangantakar masoya, musamman idan akwai matsalolin da suke gittawa ko kuma akwai rashin fahimta.

(3). Ƙarawa Soyayya Dadi:
Soyayyar dake tareda Nishadi bincike ya tabbatar da cewa tana daɗewa, domin kowa daga cikin masoyan yana jin daɗin kasancewa tareda masoyinsa da yake sa shi dariya.

(4). Bayyana So Da Nishadi:
Wasu lokuta, kalmomin barkwanci a soyayya na iya zama hanya da za'a iya amfani wajen bayyana soyayya cikin salo na barkwanci da nishadi.

Kalaman Barkwanci A Soyayya Da Zaku Iya Amfani Dasu

"Kece kayan miya ta, ba zan iya cin abinci ba in ba tareda ke ba."

Wannan kalma ta kalaman barkwanci a soyayya tana nufin cewa masoyiyarka itace gishirin rayuwarka.

"Idan soyayyarki cuta ce, wallahi bana buƙata a bani magani!"

Wannan kalma tana nuni da yadda ka kamu da soyayya kuma baka son waraka da masoyiyarka!

"Kece zuciyata, ina so ki kula kada ki fasa ta da yawan murmushinki."

Wannan zance na kalaman barkwanci a soyayya na bayyana cewa murmushin masoyiyarka tana birge ka sosai.

"Idan ke rana ce, to ni tabbas gilashi ne, saboda ba zan iya kallonki kai tsaye ba."

Itama wannan kalma ta kalaman barkwanci a soyayya tana nuna yadda masoyiyarka ke haskaka rayuwarka sosai.

"Kullum in na duba madubi, sai na dinga ganin hotonki – zuciyata ba ta gajiya da soyayyarki!"

"Da ace soyayyarki na’ura ce, da tuni ta ƙare wutar lantarkin dake cikin zuciyata saboda yawan ƙona zuciyata."

Wannan kalma ta kalaman barkwanci a soyayya ce amma tana nuna yadda soyayya keda ƙarfi.

"Idan dariyarki ruwa ce, to ni tabbas zan yi iyo a ciki har na dinga nutsewa."

"Kece 'Google' dina, saboda duk abin da nake nema a rayuwata, ina samu a wurinki."

"Idan ke kifi ce, to ni zan zama ruwa domin ba zan iya guje miki ba."

Kalma ce ta barkwanci a soyayya da ke bayyana yadda ka kamu da soyayya sosai.

"Idan zan zama kaya a kasuwa, zan roƙi Allah ki zama mai siyo ni!"

Yadda Ake Amfani da Wadannan Kalaman Barkwanci A Soyayya

Ta Waya Ko Sakon Text:
Zaka iya aika da kalaman barkwanci a soyayya ta waya ko text messages domin faranta ran masoyiyarka. 
Misali:
"Ina matukar ji dake sosai, ɗan Allah ki kula kada ki sani inyi hauka saboda soyayyarki!"

A Lokacin Da Kuna Tare:
Idan kuna tare, yin amfani da kalaman barkwanci zai saka masoyinki ko masoyiyarka yin murmushi ko ma yin dariya sosai.

Lokacin Fushi:
Idan masoyinki yana fushi, amfani da kalmomin barkwanci a soyayya na iya taimakawa wajen wanke masa ɓacin rai.

Domin Tuna Soyayya:
Lokacin ranar haihuwa, ko ranar soyayya (Valentine’s Day), ko ranar tunawa da haɗuwarku ta farko, zaka iya ƙara sakon kalaman barkwanci a cikin sakonka.

Wasu shawarwari Masu Amfani Yayin Barkwanci A Soyayya

Yanayin Masoyi:
Kamar yadda ake cewa dariya bata da iyaka, ka tabbata masoyiyarka tana fahimtar barkwancinka ba tareda jin haushi ba.

Barkwanci Mai Tsauri:
Kada ka yi amfani da kalaman barkwanci a soyayya wanda zai ɓata mata rai ko ya sa masoyiyarka ta ji rashin jin daɗi.

Barkwanci Mai Sauƙi da Fahimta:
Barkwanci mai sauƙi da nishaɗi yafi sa annashuwa a soyayya fiye da wanda keda rikitarwa.

Guji Barkwanci Mara Ma'ana:
Kada kayi barkwanci a lokacin da masoyinka ke cikin damuwa sosai ko lokacin da kake bukatar zama mai tsanani

Kalaman barkwanci a soyayya suna da matukar muhimmanci domin ƙara dangantakar soyayyarku. Kalaman barkwanci a soyayya hanya ce mai sauƙi don ƙarfafa dangantaka da saka nishadi a fuskar masoyi. Kada ka manta, koda yaushe dariya tana ƙara ƙarfafa soyayya kuma tana sa rayuwa ta zama mai matukar daɗi.

Post a Comment

Previous Post Next Post