Menene dalilin da yasa mata keyin kuka a daren farko?
Daren farko na aure musamman ga amare wani lokaci ne mai cike da tunanin yan’uwa da kuma fargaba, wanda hakan na iya kawo kuka a daren farko. Sannan kuma akwai jin daɗi, da kuma sauye-sauyen rayuwa, wanda yarinya bata zama gani ba. Ga wasu amaren, wannan rana ta farko takan iya haifar da kuka – wanda kan faru saboda dalilai daban-daban da suka shafi nutsuwar zuciya, yanayin sabo na amaraya, ko ma wasu abubuwa masu kama da haka. A cikin wannan rubutu mai taken kuka a daren a daren farko nawa ni malamar mata ta wannan gida mai aminci, zanyi bayani mai kyau akan dalilan da ke haifar da kuka a daren farko, da kuma yadda maza angwaye za su fahimci lamarin, da kuma hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da cewa daren farko ya kasance mai kyau ga duka ma’auratan, wato amarya da ango.
Ga wasu dalilan da ke sa amare kuka a daren farko
Bugun zuciya (sakamakon rashin sabo)
Amare da yawa na iya yin kuka a daren farko, saboda rashin
sabo da gurin da suka samu kansu. Wato zuciyarsu tana tattare da tunanin rayuwa
da sabuwar dangantakar da zasu kulla da ango. Kuma ayi cewa hakan na iya zuwa
da farin ciki, fargaba, har ma kuma da jin takaici. A wani bangaren na zuciyar
amarya zata dinga farinciki, wani bangaren kuma ta dinga jin takaici. Duka dai
wannan halaye suna iya faruwa da ita tun lokacin da aurenta ya matso kusa.
Domin wata amaryar tana tsanar angonta hakanan ba gaira ba dalili idan aure
yazo kusa to fa duka wannan na iya kawo kuka a daren farko.
Tsoron canji
Wasu matan kuma suna yin kuka a daren farko ne sakamakon
tsoron canjin rayuwa daga gidansu zuwa gidan aure. Wanda hakan ya na iya kawo
fargaba saboda basu san me zasu tarar da gidan auren ba. Wannan sauyi na iya
sanya mace kuka a daren farko saboda jin tsoron abin da zai faru nan gaba.
Jin kunya ko tsoro gameda jima’i
Dama dai amarya sabuwa ce bata san komai ba, ta fuskara
tarawa da miji. Ga matan da ba su saba da sha’anin jima’i ba, to wannan tsoron
yakan zama dalilin da ke sa su kuka a daren farko. Haka zalika jin kunya da
rashin sani kan iya haifar da damuwa a wannan rana.
Rashin nutsuwa da sabon muhalli
Amarya na iya jin rashin kwanciyar hankali har ta iya yin
kuka a daren farko saboda ta tsinci kanta a wani sabon wuri da ba ta saba da
shi ba. Wannan zai iya kawo mata matsanancin damuwa da fargaba. Domin nake bada
shawara cewa zaku kai diyarku gidan mijinta yana kyau ku lallasheta da kyau
saboda kowace amarya tana jin wannan a darenta na farko.
Ra’ayoyin Al’ada
Wasu al’ummomin suna da tasu irin al’adar wato dole sai sun
tabbatar da budurcin mace a wannan rana wanda hakan na iya kawo matsancin kuka
a daren farko. Wannan al'ada takan sanya wasu mata jin matsin lamba har su
fashe da kuka sakamakon tunanin abinda zai iya faruwa idan wani abu ya saba da tsammanin
iyayenta.
Jima’i
Ga amaryar data fara jima’i a daren farko, akwai yiwuwar ta
ji zafi ko raɗaɗi saboda rashin santsi da babu ko kasancewar budurci. Wannan
zai iya sa kuka a daren farko saboda jin zafi ko radadi.
Tunanin Iyaye Da Gida
Aure dai al’ada ce wacce ke nufin cewa mace za ta bar gida
da danginta domin shiga sabuwar rayuwa. Wannan na iya kawo kuka a daren farko
musamman idan mace tana da alaƙa da sabo mai ƙarfi da iyayenta.
Yadda ango ya kamata yayi domin kaucewa kuka a daren farko:
Ango akwai muhimmiyar rawar da zaka taka wajen fahimtar
lamarin kuka a daren farko da kuma tabbatar da cewa daren farko ya kasance
lokaci mai kyau kai da amaryarka. Ga wasu shawarwari da zaka iya amfani dasu:
Ka Nuna Hakuri Sannan Ka Fahimceta
Ka fahimci cewa kuka a daren farko wani abu ne na al’ada da
zai iya faruwa saboda dalilai daban-daban. Kada ka tsawatarwa matarka ko ka
nuna mata cewa kana fushi; a maimakon haka, ka kasance mai hakuri da kwantar da
hankalinta domin yanzu kai kadai ta sani.
Kayi Magana Da Ita
Idan kaga amaryarka tana kuka a daren farko tofa dole akwai
dalili, saboda haka yanada kyau ka tambayeta cikin natsuwa ko tana da abinda
yake damunta kuma wani abu da take so ta faɗa. Wannan zai bata damar bayyana
abin da ke damunta kuma ya rage mata nauyin da take ji a zuciyarta. Kaga kenan
cikin sauki zaka iya shawo kan matsalar kuka a daren farko ba tareda wata
wahala ba.
Ka Ba Ta Lokaci
Idan matarka tayi kuka a darenta na farko, to yana da kyau
ka bata lokaci domin ta dawo da natsuwarta kafin kuma ka yi ƙoƙarin ci gaba da
tattaunawa da ita ko kuma yin wani abu.
Guji Takurawa Amarya
Kada ka yiwa amarya matsin lamba musamman game da jima’i a
daren farko. Domin gujewa yin kuka a daren farko to kada ka takura yarinya
domin yin jima’I. Idan kayi mata haka to wannan zai rage tsoro da damuwar da
take ji.
Hanyoyin da zasu taimaka wajen magance kuka a daren farko:
Shiryawa
Ango kana da alhakin tattauna da matarka akan yadda za ku shawo
kan fargaba da damuwar da zata iya tasowa a daren farko. Wato dai a takaice zan
iya cewa magana a tsakanin ma’aurata zata taimaka wajen rage duk wasu matsaloli
daka iya haifar da kuka a daren farko.
Nutsuwa Da Fahimtar
Daren farko ba lokaci ne na takura ba. Ka tabbatar kun
fahimci juna da amarya sannan kuma ku kasance masu sauraron wato bi a hankali
yayin saduwa da juna.
Goyon Baya
Ango ka kasance mai kwantar da hankalin matarka musamman a
daren farko, wato iya nufin ka lallabata sannan kasha dadi, a ci gurasa yadda
ya kamata sannan itama ka jiyar da ita sabon dadin da bata taba jin irinsa ba a
rayuwarta gaba daya. Ka goyi bayan matarka akan sha’awarta domin wasu amaren
wallahi da jaraba suke zuwa don haka sai kabi a hankali kuma ka tabbatar ka
bata duk abinda take so koda bata tambaya ba.
Tattaunawa
Idan kun fahimci juna da yarinyar da zaka aura, tofa zaku
iya shawo kan matsaloli da dama balle kuma karamin abu kuka a daren farko.
Kafin daren farko, yana da kyau ma’aurata ku tattauna kan halayen juna da yadda
za su gina kyakkyawar dangantaka mai ɗorewa.
Kammala wannan rubutu nawa
Kuka a daren farko wani abu ne da ke faruwa ga amare da yawa
saboda dalilai daban-daban kamar tsoro, damuwa, da kuma rashin sabo. Duk da
haka, idan akwai fahimta, goyon baya, da kwantar da hankali, za a iya rage
wannan kuka a daren farko wanda hakan zai saka daren farko ya kasance lokaci
mai daɗi da farin ciki.
Ku tuna cewa, hakuri da soyayya
suna da muhimmanci wajen gina dangantaka mai ƙarfi. Wannan zai tabbatar da cewa
daren farko ba kawai lokaci ne na fargaba da kuma jindadi ba, a’a lokaci ne na
ƙulla kyakkyawar dangantaka da za ta ginu har abada.