Maganin Sanyi Na Budurwa:
Sanyi na budurwa wata cuta ce dake damun mata da dama a wannan zamani, musamman matan da ba su taɓa haihuwa ba wato yan'mata ko mace budurwa. Wannan cuta ta sanyi wacce a turance ake cewa infection na iya shiga jikin mace sakamakon jima’i (STDs), cututtukan al’aura, ko kuma rashin tsafta. A cikin wannan blog post namu na wannan rana mai taken maganin sanyi na budurwa zamu tattauna dalilan dake kawo sanyi na budurwa, alamominsa, da hanyoyin magance shi ta hanyar magunguna na asibiti dama na gargajiya gaba ɗaya.
Menene Sanyi Na Budurwa?
Sanyi na budurwa yana nufin duk wasu cututtuka dake shafar farjin ɗiya mace, wanda ke haddasa mata jin zafi, ƙaiƙayi, da fitar farin ruwa mai wari ko mai kauri. Sanyi a yawancin lokuta na iya shafar lafiyar mace, musamman idan ba'a magance shi da wuri ba.
Menene Dalilan Dake Kawo Sanyi Na Budurwa?
Akwai dalilai daban-daban dake haddasawa budurwa wannan matsala ta infection, waɗanda suka haɗa da:
(*). Cututtuka Masu Yaɗuwa Ta Hanyar Jima’i (STDs) – Kamar su gonorrhea, chlamydia, da trichomoniasis. Matsawar budurwa ta sadu da namiji mai waɗannan cutuka dana lissafa a sama to tabbas zata iya kamuwa da cutar sanyi na budurwa.
(*). Ciwon Infection a Farji – Mace na iya kamuwa da sanyi sakamakon rashin tsafta musamman ga kayan ƙasa irinsu pant da bireziyya ko kuma amfani da kaya masu datti.
(*). Canjin Hormone – Rashin daidaiton sinadarin hormone a jikin ɗiya mace na iya haifar da rashin lafiyar farji.
(*). Amfani da Magunguna Barkatai – Yawan yin amfani da wasu magunguna na iya kawo rashin daidaito a jikin mace, wanda ke haddasa fitar farin ruwa mai wari daga gabanta.
(*). Amfani da Kayan Mata – Amfani da pads, pant, ko sabulu marasa tsafta na iya haddasa sanyi na budurwa.
Menene Alamomin Sanyi Na Budurwa?
1. Fitar farin ruwa mai wari daga farji
2. Zafi ko ƙaiƙayi a farji
3. Jin zafi yayin fitsari
4. Yawan yin fitsari
5. Ciwon ciki
6. Ƙumburin farji
Hanyoyin Da Ake Magance Sanyi Na Budurwa
Akwai hanyoyi guda biyu wanda aka fi amfani dasu domin yin maganin sanyi na Budurwa: Shine ta amfani da maganin asibiti da magungunan gargajiya.
1. Maganin Asibiti
Ina bayar da shawarar cewa da an fuskanci sanyi yayi tsanani, tofa yana da kyau a ziyarci likita da gaggawa domin yayi gwaji sannan ya bayar da maganin sanyi na budurwa da ya dace. Wasu daga cikin magungunan asibiti da ake amfani dasu sun haɗa da:
Antibiotics kamar azithromycin ko doxycycline (domin STDs)
Antifungal creams kamar fluconazole idan ciwon fungus ne
Metronidazole ko tinidazole domin cutar trichomoniasis
2. Magungunan Gargajiya
Idan ana bukatar yin amfani da hanyoyin gargajiya ne kuma, akwai wasu daga cikin magungunan da aka fi amfani dasu waɗanda suka haɗa da:
Shan kunun Aya Da Garin Habbatus-sauda – Suna taimakawa wajen tsabtace farji.
Ruwan Zogale – Shi kuma ana shan shi domin tsaftace ciki.
Lemu Da Zuma – Suna taimakawa kwarai da gaske wajen rage ciwon ciki da maganin sanyi na budurwa wato infection.
Garafuni Da Ganyen Magarya – A tafasasu a sha domin maganin cutar infection.
Yadda Ake Kare Kai Daga Cutar Sanyi Na Budurwa
A kiyaye tsafta sosai
Kada ayi amfani da kayan wanka masu illa ga farji
A guji amfani da kaya masu datti
A guji yin jima’i da mai dauke da cutar infection
Shan ruwa mai yawa domin cigaban lafiyar jiki
Maganin sanyi na budurwa na iya zuwa daga masana koda ba likitoci bane, domin ilimi kogi ne. Yana da kyau a sani cewa sanyi na budurwa matsala ce da ke iya hana mace jin daɗin rayuwa, kuma idan ba'a magance shi da wuri ba, na iya haddasa matsaloli kamar rashin haihuwa. Yin amfani da magunguna na asibiti ko na gargajiya suna taimakawa sosai wajen warkar sanyi na budurwa. Duk da haka, mafi muhimmanci shine a kiyaye tsafta da kuma kula da lafiyar jiki a kullum da koda yaushe.
Tags
Taka Lafiya