Sakon Soyayya Na Dare:
Soyayya tana da matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam. Yana da kyau ka nuna kulawa da kauna ga masoyiyarka ko masoyinki a kowane lokaci, musamman ta hanyar tura sakon soyayya na dare yayinda hankalin kowane ɗan Adam yake nutse. Idan kana son koda yaushe masoyiyarka taji ka a zuciya da tunaninka kafin tayi barci, to ka sani rubuta mata sakon soyayya na dare zai taimaka sosai wajen yin hakan. Haka zalika kema yar budurwa idan kina son sahibinki ya dinga tunawa dake a koda yaushe to da bukatar ki tura masa sakon soyayya na dare a kowace rana.
A cikin wannan post nawa ni malamin soyayya na wannan gida, zanyi iya bakin ƙoƙarina domin raba muku wasu kyawawan sakon soyayya na dare da zasu sa zuciyar masoyanku ta cika da farin ciki da kewarku.
Meyasa Tura Sakon Soyayya Na Dare Yake Da Muhimmanci A Soyayya?
Yana Kara Dankon Soyayya: Lokacin da kike ko kake aikawa da sakon soyayya da dare kafin barci, yana sanya masoyinki yaji dadin soyayyar da kike nuna masa hakan ko zai saka ya dinga kewarki har zuwa wayewar gari.
Yana Samar Da Nutsuwa: Sakon soyayya na dare mai dadi yana kwantar da hankalin saurayinki ko budurwarka kuma yana saka su barci mai dadi.
Yana Kawo Kewar Masoyi: Lokacin da kika aika da sakon soyayya na dare mai dadi, babu shakka hakan zai sanya masoyinki yin barci tareda kewarki.
Jerin Gwanon Sakon Soyayya Na Dare
1. Kalaman Soyayya Na Dare Zuwa Ga Budurwa Ko Matar Aure
"Kafin ki rufe idonki ki yi barci, ki sani cewa ina kaunarki fiye da yadda kalmomi zasu iya bayyanawa. Ki yi barci cikin koshin lafiya, masoyiyata."
"Ko da dare yayi duhu, soyayyata gareki tana haskaka zuciyata kamar tauraron dare. Ki kwanta cikin aminci, gimbiya ta."
"Ina miki fatan barci mai cike da nishadi. Koda yaushe Ina nan a zuciyarki, kamar yadda kike a tawa."
2. Sakon Soyayya Na Dare Zuwa Ga Saurayi Ko Mijin Aure
"Ina fata ka kasance cikin kwanciyar hankali masoyina. Sannan Ina maka fatan kana jin kaunar da nake maka duk lokacin da ka rufe idonka."
"Ina sonka fiye da komai a duniya. Ka yi barci lafiya, hasken zuciyata."
"Habeeby kada ka manta, kai ne mafarkin zuciyata. ka yi barci lafiya masoyina."
3. Sakon Soyayya Na Dare Masu Rikitarwa
"Idan kika rufe idonki, ki tuna cewa ina nan kusa da ke, a cikin zuciyarki. Haka zalika idan kin buɗe ma ina tare da ke, Ina yi miki fatan mafarki mai dadi."
"Daren yau ya fi kowanne kyau, saboda yana dauke da soyayyata gareki. Ki yi barci cikin aminci, annurin kyakkyawar zuciyata."
Yadda Zaku Rubuta Sakon Soyayya Na Dare Masu Kyau
Siddabaru: Zaki iya amfani da duk wata kalma mai dadi wacce kika san zata sanya masoyinki cikin farin ciki, koda kuwa karya ne abun bukatar kawai shine ki zama silar dorewar farin cikinsa hakan kuwa zai sanya koda yaushe ya kasance tareda ke. Haka zalika kai ma saurayi kayi amfani da siddabarun kalamai na sakon soyayya na dare domin saka babynka cikin farin ciki.
Sanya Sunansa Ko Sunanta: Yin rubutu wani lokacin da sanya sunan masoyi yana taimakawa kwarai da gaske, domin yin haka yana kara darajar sakon soyayya na daren da zaka tura. Misali: "Fatima, ina son ki. Ki yi barci cikin koshin lafiya."
Sanya Fatan Alheri: Irin su "Ka yi mafarkin mai kyau da armashi" ko "Allah ya kare ka uban yayana" domin hakan suna kara nishadi da jin dadi.
Sakon soyayya na dare wata hanya ce mai kyau domin nuna kauna da kulawa ga masoyi. Duk da cewa suna da saukin rubutawa, kar ayi garaje wajen rubutun zai fi kyau a tsaya a tsara sannan a rubuta. Idan kana son tabbatar da cewa masoyiyarka ko masoyinki ta kasance tana yawan begenka to kada ka manta da aikawa da sakon soyayya na dare masu dadi tun kafin dare ya yi nisa masoyin yayi bacci.
Tags
Soyayya