Sunayen Masoya da Faransanci:
Soyayya babbar magana ce a dukkan zuciyar masoyi, wacce yake kulawa da girmamawa da ita a koda yaushe musamman idan yana son masoyiyarsa. Sunayen soyayya da faransanci zasu yi muku amfani mara iyaka domin zasu ƙara janyo muku masoyinku kusa. Kun san meyasa nace zasu muku amfani? yin amfani da sunayen soyayya da faransanci zasu nunawa masoyinki ko masoyiyarka cewa Eh' lallai kana sonta. Musamman Idan kana yawan amfani dasu.
Kowa ya sani cewa zancen soyayya zance ne mai daɗi wanda masoya ke amfani dashi domin nuna kulawa da kuma son ganin masoyinsu cikin nishaɗi da farinciki. Kuma yaren da ake amfani dashi wajen bayyana soyayya yana da matukar tasiri ga zukata musamman idan ka iya bayyanasu. Tom bari mu koma kan batun daya kawo mu kai tsaye 'Yaren Soyayya da Faransanci ana kiransa da "La Langue de l'Amour" wato harshen masoya ga malam bahaushe. Lafazin sunayen soyayya da faransanci masu daɗi ne wanda hausawa da yawa musamman yan'mata suke son yin amfani dasu.
Idan kina da masoyi ko kana da masoyiya, ko kuma kana son ƙara shigar da sabbin kalmomi domin ƙara inganta soyayyarka, to fa ina maka albishir cewa kazo inda ya dace domin wannan rubutun zai taimaka maka wajen koyon sunayen masoya da Faransanci da kuma yadda ake amfani dasu.
Meyasa Faransanci Yake Da Kyau A Soyayya?
Sunayen masoya da Faransanci suna taka gagarumar rawa wajen faranta ran masoyi domin wani da kin kira shi da irin wannan suna zai yi miki murmushi sannan kuma ya soma tambayarki me hakan yake nufi.
Faransanci yare ne da ke da kyawawan lafazi, kuma yana ɗaya daga cikin yarukan da ake kara kulla soyayya dasu a duniya. Kalmomin da ake amfani da su wajen kiran masoyi suna da kyawun ma'ana kuma suna da sauƙin faɗi. Idan kin kira masoyinki da sunan to tabbas babu tantama hakan yana ƙarfafa dangantaka kuma yana nuna yadda kike so da ƙaunar masoyi.
Ga jerin sunayen masoya da Faransanci da kuma ma'anarsu da Hausa:
Mon Amour (Mon a-moor) – Abun Sona
Wannan kalma ce ta soyayya da ake amfani da ita sosai don kiran masoyi kamar ace 'Babe' da harshen turanci. Kuma ana iya amfani dashi ga namiji ko mace.
Mon Chéri (Mon she-ree) – Masoyina (Namiji)
Wannan kalmar tana nufin “Masoyina” ga namiji. Idan kina kiran saurayinki ko mijinki da Mon Chéri, yana nuna kulawa da kuma kauna.
Ma Chérie (Ma she-ree) – Masoyiyata (Mace)
Wannan shine nau’in sunan soyayya na mace wato Mon Chéri. Ana amfani dashi don nuna soyayya ga budurwarka ko matarka ta aure.
Mon Bébé (Mon beh-beh) – Jaririna / Babyna
Kamar yadda ake amfani da Baby a Turanci, Faransawa suna amfani da Mon Bébé don kiran masoyinsu cikin kulawa.
Mon Cœur (Mon kur) – Zuciyata
Wannan suna yana nufin “Zuciyata.” Idan ka kira masoyiyarka Mon Cœur, yana nufin cewa shine abinda zuciyarka ke bugawa saboda shi.
Mon Trésor (Mon tre-zor) – Dukiyata
Wannan suna yana nufin “Dukiyata” ko “Gemu na.” Yana nuna yadda kake daraja masoyi fiye da komai.
Mon Ange (Mon anj) – Tauraruwata
Idan kina kiran masoyinki Mon Ange, yana nufin cewa kina ganinshi ko ita tamkar tauraruwa ce a rayuwarka.
Ma Belle (Ma bel) – Kyakkyawata
Daga cikin sunayen soyayya da faransanci ana amfani da sunan Ma Belle don kiran mace kyakkyawa. Idan kana son nuna jindaɗi akan kyawunta, wannan suna yana da kyau da wannan wajen.
Mon Beau (Mon bo) – Kyakkyawana
Wannan shine nau’in suna na namiji wato Ma Belle. Idan mace tana son kiran saurayinta ko mijinta kyakkyawa, tana iya cewa Mon Beau.
Mon Lapin (Mon la-pan) – Zomona
Wannan suna ne mai daɗi da kuma nishaɗi. Koda yake yana nufin zomo, amma dai ana amfani dashi a matsayin suna mai daɗi na soyayya da faransanci.
Ma Puce (Ma poos) – Karamin Ƙwarona
Duk da cewa Puce na nufin ƙaramin ƙwaro, amma Faransawa suna amfani dashi don nuna ƙauna mai tsanani ga masoyansu.
Mon Chaton (Mon sha-ton) – Kyanwata
Wannan suna yana nufin kyanwa ko mace karama, kuma ana amfani dashi don bayyana soyayya mai kyau ga masoyi.
Mon Loup (Mon loo) – Gawurtaccena (Zaki)
Idan kina son kiran masoyinki suna mai nuna ƙarfi da nuna jarumtaka, zaki iya amfani da Mon Loup wanda yake nufin zaki ko sadauki.
Mon Rêve (Mon rev) – Burina / Mafarkina
Wannan suna yana nufin mafarki ko burina wanda nake son cimmawa, yana nuna cewa masoyinki shine abin da zuciyarka take mafarkinsa.
Mon Soleil (Mon so-lay) – Ranata
Idan kina kiran masoyinki da Mon Soleil, yana nuna cewa shine hasken rayuwarki, kamar yadda rana ke haskaka duniya.
Yadda Ake Amfani Da Wadannan Sunayen Soyayya da Faransanci A Rayuwar Soyayya:
Sakon Soyayya:
Idan kina rubuta sakon soyayya ga masoyinki, zaki iya amfani da waɗannan kalmomin domin ƙara jan hankalinsa a soyayyarki. Misali:
"Bonsoir, Mon Amour! Ina fata kana lafiya yau. Ina matukar kewanka!"
Kiran Waya:
Lokacin kiran waya, zaki iya amfani da wannan suna na jerin sunayen soyayya da faransanci domin yin kiran wayan:
"Salut, Ma Chérie! Yaya yau?"
Lokutan Farin Ciki:
Idan kuna tareda masoyinki, yin amfani da irin waɗannan sunayen na ƙara jindaɗi da ƙara muku kusanci.
Kirkirar Sunaye Na Musamman:
Zaku iya haɗa sunaye biyu ko ƙirƙirar naku na musamman domin masoyanku daga cikin wadannan sunayen soyayya da faransanci Misali:
"Mon Bébé Soleil" (Babyna haske) ko "Ma Belle Ange" (Kyakyawar Tauraruwata).
Sunayen Masoya da Faransanci suna da amfani domin soyayya tana buƙatar kulawa da ƙananan abubuwa sababbi. Kamar yadda kalmomin da ake amfani dasu wajen soyayya suke da muhimmanci haka masoyin keda muhimmanci. Yaren Faransanci kuwa yana da kalmomi masu daɗi da ma'ana da zasu ƙara ɗaukaka soyayyarku. Wato yallabai kai saurayi ne ko budurwa, amfani da irin waɗannan sunayen zai sa dangantakarku ta ƙara ƙarfi da jin son kasancewa da juna.
Tags
Soyayya