Zubar da ciki da gishiri: Illolin Amfani da Hanyoyin Gida Wajen Sauke Ciki:
A gaskiya ayi sani cewa zubar da ciki ba batun da ya kamata a dauka da wasa bane, kuma amfani da hanyoyin gida kamar gishiri ko wasu sinadarai na gida na iya jawo matsaloli masu tsanani ga lafiyar mace. Wannan blog post ɗin nawa na yau zai yi bayani kan illolin amfani da hanyoyin gida wajen zubar da ciki da gishiri, muhimmancin neman taimakon likita, da kuma wasu dabaru da zaki iya amfani dasu domin shirya kanki cikin aminci.
Shin Zai Yiwu a Zubar da Ciki da Gishiri?
A fannin likitanci, babu wata hujja ko bincike daya tabbatar da cewa zubar da ciki da gishiri na aiki. Duk da cewa wasu mutane suna gwada wannan hanya, to ayi sani cewa hakan yana da matukar haɗari sosai ga lafiyar mace. Amfani da zubar da ciki da gishiri ko wasu kayan gida don zubar da ciki ba hanya ce mai lafiya ko inganci ba, kuma yana iya kawowa mace matsaloli kamar haka:
(*). Zubar da Jini Mai Yawa: Amfani da hanyar zubar da ciki da gishiri na iya haddasa matsalar zubar da jini daga gaban mace wanda ka iya haddasa barazana ga rayuwa.
(*). Cutar Mahaifa: Zubar da ciki da gishiri ko wata hanya ta gargajiya ba bisa ka'ida ba na iya haifar da ciwon mahaifa, wanda zai iya jawo rashin haihuwa a nan gaba.
(*). Infection (Cutar Sanyi): Amfani da hanyoyi domin zubar da ciki wanda basa da wani tushe mai kyau na iya haifar miki da cutar sanyi ko amfani da hanyoyin gida yana iya sa mace ta kamu da cututtuka masu tsanani kamar tetanus ko sepsis.
(*). Mutuwa: A wasu lokutan ma kokarin zubar da ciki da gishiri ba tareda taimakon likita ba cikin gaggawa yana iya kaiwa ga mutuwar mace.
Muhimmancin Neman Taimakon Likita:
Idan mace tana cikin wani hali da take buƙatar kula da juna biyu ko hanyar da zata iya zubar da ciki, to ya kamata ta nemi taimakon likita ko wani ƙwararren ma’aikacin lafiya. Likitoci zasu iya bayar da shawara kan mafi kyawun hanya data shafi zubar da ciki, ko wata matsalar lafiya, ba tareda jefa mace cikin haɗari ba.
A cikin ƙasarmu Najeriya, dokokin zubar da ciki suna da tsauri sosai, sai dai idan ya zama tilas ko idan rayuwar mace tana cikin haɗari. Amma idan akwai wata damuwa dake damun mai ciki, neman shawara daga ƙwararren likita shine hanyar tabbatar da lafiya ga kowace mace mai ciki.
Hanyoyin Da Za'a Iya Bi Domin Kariya:
Idan kin tabbatar da cewa baki shirya samun ciki ba, akwai hanyoyin da zaki iya amfani da su domin kiyaye ɗaukar ciki cikin koshin lafiya da lumana:
(*). Amfani da Kayan (Contraceptives): Ba bukatar zubar da ciki da gishiri domin wadannan sun haɗa da kwayoyi, allurai, ko na'urar IUD da ake sakawa a mahaifa kinga kenan ba zaki ɗauki ciki ba tun da farko.
(*). Shawara da Iyali: Kuyi shawara kai da iyalinka akan tazarar haihuwa ko a nemi shawara daga ƙwararrun ma'aikatan lafiya kan yadda za'a bi wani tsari na iyali domin tazarar haihuwa.
(*). Sanin Lokacin Haihuwa: Mata da yawa sun san duk wasu alamu na idan suna dauke da juna biyu tun kafin ya kai wani munzali, domin hakan zai baki dama kiyi abinda ya kamata tun kafin lokaci ya kure.
(*). Bin Tsari Mai Kyau: Zaɓar tsari mai Kyau shine yafi dacewa don kauce wa haɗari ko wani sakamakon da ba a shirya masa ba.
Illar Amfani Da Zubar da ciki da gishiri ko kayan Gida:
Batun amfani zubar da ciki da gishiri ko wasu sinadarai na gida wajen zubar da ciki abu ne wanda yake faruwa ba tareda ilimi ba, domin haka a kiyaye lafiya.
(*). Ilmantarwa da Fadakarwa: Ya zama wajibi ga gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu su gudanar da wayar da kan jama’a kan muhimmancin neman taimakon likita da kuma hanyoyin tazarar haihuwa domin gujewa zubar da ciki da gishiri.
(*). Samun Sauƙin Kaya: Samar da kayan tazarar haihuwa daga gwamnati domin samun sauƙi zai taimaka wajen rage yawan mace-macen da suka shafi zubar da ciki ba bisa ka’ida ba.
Ku Sani Cewa
Zubar da ciki da gishiri ko amfani da hanyoyin gida kamar lalle don zubar da ciki yana da haɗari sosai ga rayuwar mace. Ya kamata ki nemi taimakon likita don magance kowace matsala da ta shafi ciki. Hakanan, yin amfani da dabarun tazarar haihuwa zasu taimaka wajen hana samun ciki da ba a shirya ba cikin lafiya da kwanciyar hankali.
Ku tuna cewa, rayuwa tanada muhimmanci. Kada ku bar rashin sani ya jefaku cikin haɗari. Duk lokacin da kuka shiga damuwa, zai fi kyau ku nemi taimako daga masana lafiya shine mafita sahihiya.
Tags
Taka Lafiya